|

44 Reasons to Re-elect President Muhammadu Buhari in Hausa

Yanzu shekarar zaben 2019 ce, a shekarar da yan nijeriya zasu zabi wanda zai mulke su na tsawon shekara hudu a Irin wannan lokacin ne ya kamatta kuma mu waiwayi baya dan fahimtar daga Ina muka fito mu kuma duba a ina muke yanzu, kuma mu dubi Ina muke tunkara. Mu kuma san me Muke so.

Tafiya mai kyau itace wacce acikinta akwai nasara da kuma gyaran kura kurai ta yanda acikinta zamu gujewa fadawa cikin kura kuran wadanda suka gabace mu.

Kafin zuwan wannan gwamnatin ta buhari nijeriya tana fuskantar kalubale da yawa na rashin tabbas, yan taadda sun zamo acikin mu bisa tilas, kullum tsoro ne a zukatanmu kayayyakin more rayuwa ba’a maganarsu, a lokacin yankin arewa maso yammacin kasa baya shiguwa, kuma wasu sassan kasar nan suka zama mazaunin yan gudun hijira, cin hanci da rashawa ya yi mana katutu, ga matsalar karanci ayyukan yi jin dadin rayuwa yayi karanci hadin kan mutanen kasa ya zama abu mai wahala.

A yanza haka da iskar canji ta kada kuma mu ka bita, yanza muna murmure wa daga matsalolin mu na baya, shugaban kasa Muhammad buhari ya bamu karfin gwaiwa ya fitar damu daga rana zuwa inuwa, acikin shekaru uku da rabi kacal buhari ya canja mana rayuwa, ya sa’mun san darajarmu ya farfado da ita, a yanza mun samu tsaro fiye da a baya.
A cikin shekaru hudu na gwamnatin buhari a yanzu rayuwar mu ta canja daga wahala zuwa jin dadi kuma muna more wa romon dimokradiyya.

Yanzu nijeriya mun samu makoma mai kyan a mulkin buhari na shekaru uku da rabi kacal, shiyasa muke fatan mu sake baiwa buhari wata dama yayi wasu shekaru hudun dan cigaban aiyukan a kasar nan, mu zabe shi karo na biyu ya zamanto yayi mulkin.

kasar mu 4+4 ne shekara 8 kenan, dan cigaba aiyukan alkairin daya faro adan haka ne ma muke fatan bayyana mukuwasu dalilai guda 44, daya sanya yake da kyawun gaske mu sake zabar shugaba buhari a zagaye na biyu a matsayin shugaban kasar mute nijeriya.

Signed

Shugaban, WEBELIEVE

 

 

44 REASONS TO RE-ELECT PMB - HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Featured Posts

44 Reasons to Re-elect President Muhammadu Buhari in Yoruba

2019 Agenda, Politics Talk, Social Media, The Stories

Ọdun idibo de bawa, 2019 nigba ti awon eniyan Naijiria ma pinnu eni ti o ma gba agbara ijoba fun ọdun mẹrin to nbo. O jẹ akoko ti a wo eyin lati wo ibi ti a ti n bo, wo ni bayi lati wa ibi ti...

44 Reasons to Re-elect President Muhammadu Buhari in Hausa

Yanzu shekarar zaben 2019 ce, a shekarar da yan nijeriya...

The Buhari Effect

When the 2003 elections results were announced, the...

44 Reasons to Re-elect President Muhammadu Buhari

It is an election year, 2019 when Nigerians decide who...

Buhari Administration Projects in North East Nigeria

1. Dualisation of Shuarin-Azare section of...